1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Wasu limaman Coci sun goyi bayan auren jinsi

Ramatu Garba Baba
May 12, 2021

Ra'ayoyi sun sha banbam kan amincewa da aure ko mu'amala ta jinsi daya da wasu limaman Cocin Katolikan Jamus suka yi. Da dama na ganin hakan ya sabawa ka'idar darikar Katolika.

Estland Tallinn Symbolbild männliches Paar
Hoto: Lev Dolgachov/Zoonar/dpa/picture-alliance

A Jamus, Limaman Cocin Katolika sama da dari ne suka amince tare da bayar da goyan bayansu ga masu mu'amala ko auren jinsi daya. Batun dai, ya dauki hankulan duniya inda wasu ke yabawa da matakin, wasu kuwa na ganin ya sabawa ka'idar darikar Cocin Katolika. Kawo yanzu dai, mujami'u Jamus ba su aminta da hakan a hukumance ba, hakazalika fadar Vatikan ta haramta auren jinsi.

A daya bangaren kuwa, Ministan harkokin wajen Jamus, Heiko Maas zai gana yau, da Fafaroma Francis a fadar Vatikan, ganawar da za su ta sirri, za ta mayar da hankali kan batun cin zarafin yara kanana ta hanyar lalata da ake zargi yayi kamari a tsakanin mayan limaman Cocin.

Maas bayan isa birnin Rome, ya sheda ma manema labarai cewa, ya damu kwarai da wannan batu zai kuma so ya ji, matakin da Fafaroman ke shirin dauka kan matsalar. Ministan na Jamus, shi ne na farko da ke irin wannan ganawa da shugaban Cocin Katolikan a tsawon shekaru ashirin da suka gabata.