Martani kan harin asibitin al-Ahli-Arab a Gaza
October 18, 2023Yayin da ake kwashe gawarwaki daga asibitin da hare haren rokokin suka ragargaza a Gaza, ma'aikatar lafiya a yankin ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon harin ya haura mutum 500. Tuni shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya zargi Isra'ila da kai harin da nufin yin kisan kare dangin da zai razana mazauna yankin domin yin kaura
‘Ya ce muna bukata a wannan yanayi mai matukar muni, Majalisar Dinkin Duniya ta hukunta isra'ila 'yar mamaya bisa wannan mummunan kisan kiyashin da ta yi wa marasa lafiya da danginsu da likitoci da ma'aikatan jinya. Muna bukatar samun kariya ta dakarun Majalisar Dinkin Duniya. Ba za mu fice mu bar musu kasarmu ba har abada.”
Karin Bayani:Damuwa kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa
To sai dai a hannu guda, Firaim ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya zargi kungiyar Hamas da kai harin da ya ce yayi kama da irin hare haren kan mai uwa da wabi da kungiyar ta kai mata kwanaki 11 da suka gabata:
"Abun da ya faru yau shine irin abin da ya faru a Isra'ila kwanaki 11 da suka gabata.Yan ta'addar da ke kokarin harba rokoki kan Isra'ila ne kaikayi ya koma kan mashekiya, rokokin suka kauce suka fada kan wannan asibitin, lamarin da ke nuni ga muhimmancin samamen da muke yi na share irin wadannan 'yan ta'addan daga doron kasa.”
Shi ma ministan tsaron kasar ta Isra'ila, Yair Laveed, nesanta dakarunsa ya yi daga wannan mummunan harin inda ya ke cewa:
"A ci gaba da aikin ta'addancin da Hamas ke yi, rokokinta marasa linzami, sun fada kan asibitin da ya halaka majinyata da masu neman mafaka. Wannnan shi ne sakamakon barin makamai a hannun kungiyar 'yan ta'adda, za ta kashe wadanda ta ke dauka makiya, kafin ta kashe kanta dama masoyanta.”
Tuni dai shugabanin larabawa suka yi tofin Allah tsine da wannan harin, inda Sarkin Jodan da shugaban Falasdinawa suka soke ganawar da aka shirya za su yi da shugaban Amurka Joe Biden da ke ziyara a yankin,don abin da suka kira, goyan baya ido rufe da yake ci gaba da yi wa Isra'ila.
Zanga zangar nuna damuwa da wannan mummunan harin ta barke a garuruwa da dama na kasashen larabawa da na musulmi.