1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yaya rikicin Gabas ta Tsakiya zai kaya?

Suleiman Babayo LM
October 2, 2024

Ana ci gaba da mayar da martani game da hare-haren rokokin da Iran ta kaddamar kan Isra'ila, inda manyan kasashe ke jaddada matsayinsu na cewa Isra'ila na da damar kare kanta.

Gabas ta Tsakiya | Rikici | Iran | Isra'ila | Lebanon | Hare-hare | Martani
Iran din dai ta ce rokokin da ta harba ISra'ilan somin tabi neHoto: dpa/picture alliance

Tuni manyan kasashen kamar Birtaniya firaministan kasar Keir Starmer ya tabbatar wa takwaransa na Isra'ila Benjamin Netanyahu cikakken goyon bayansa, tare da yin tir da matakin Iran na kaddamar da hare-haren rokokin. Firaminista Starmer ya ce babu wanda zai amince da matakin Iran na harba makamai masu linzami kusan 200, kuma abin da mahukuntan Iran suke bukatar gani shi ne kassara fararen hula na Isra'ila. Shi ma Firaminista Anthony Albanese na kasar Australiya, na cikin shugabannin kasashen duniya da suka tir da matakin na Iran. cikin sanarwar da ministan harkokin wajen Isra'ilan Israel Katz ya fitar, Isra'ila ta nuna mamakin yadda sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gaza yin tir da wannan hare-hare na Iran tare da haramta masa sake shiga kasar.

Tuni Isra'ila ta bayar da umarnin neman mafaka a wuraren ko-ta-kwana mafi kusaHoto: Tomer Appelbaum/REUTERS

Gwamnatin Isra'ila ta yi barazanar cewa za ta dauki fansa game da makaman roka da Iran ta harba zuwa kasar. A hannu guda kuma Iran din ta ce muddun Isra'ila ta yi yunkurin kai mata hari, za ta lalata kayayyakin more rayuwan Tel Avivi din. Wannan rikici na yankin Gabas ta Tsakiya da tsoron yuwuwar barkewar yaki a yankin, ya janyo tashin farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya. Muddun wannan rikici na yankin Gabas ta Tsakiya da ake fargabar yiwuwar rincabewarsa ya gawurta farashin danyen man fetur zai ci gaba da tashin gwauron zabi, saboda tasirin kasashen wajen fitar da man fetur zuwa kasashen duniya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani