1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Martani kan hukuncin Joseph Kabila

Zanem Nety Zaidi | Mouhamadou Awal Balarabe SB
October 1, 2025

A Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, hukunci kisa da aka yanke wa tsohon Shugaban Joseph Kabila ya janyo cece-kuce a tsakanin 'yan siyasa. Babbar kotun soji ta kasa ta same shi da laifin goyon bayan tayar da zaune tsaye.

Tsohon Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Tsohon Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Jospin Mwisha/AFP

Babbar kotun soji ta kasa ta same shi da laifin marar hannu wajen tada zaune tsaye da 'yan tawayen M23 suka yi a gabashin DR Kwango.

Babban alkalin kotun sojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya yanke hukuncin inda ya ambato sashe na bakwai na kundin hukunta laifukan soji, wajen yanke wa Joseph Kabila hukunci mafi tsanani a kasar wato na kisa.

Yanke hukuncin

Kotun soja a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango lokacin hukuncin tsohon Shugaba Joseph KabilaHoto: Samy Ntumba Shambuyi/AP Photo/picture alliance

Ko da yake dai a bayan idonsa aka gudanar da shari'ar saboda yana gudun hijira, amma kotun ta soji ta ce ta samu tsohon shugaban Kabila da laifin "cin amanar kasa" da " laifuffukan yaki ". Sai dai  Souzy Kisuki, mai fafutukar kare hakkin dan Adam ta nuna tababa kan hukuncin, inda ta kasance a sahun wadanda suke ganin cewar ba za a iya zartar da kisan ba.

Sai dai mukarraban tsohon shugaban kasa Joseph Kabila, na ganin cewa wannan hukunci kisa da aka yanke wa gwaninsu zai iya karar tsaye ga duk wani yunkurin diflomasiyya da ake yi na samar da zaman lafiya da dawwamammiyar hanyar warware rikicin da ya dabaibaye gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Martani bayan hukuncin

Tsohon Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: TONY KARUMBA/AFP /Getty Images

Hukuncin da babbar kotun sojin Kwango ta yanke, ya ba da umarnin kamo Sanata Joseph Kabila nan take, bayan da aka same shi da daukacin laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa. Amma masanin siyasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Farfesa Bob Kabamba, ya ce wannan hukunci ne da ke da wahalar aiwatarwa a Kwango saboda ba farau ba ne

Baya ga hukuncin kisa da aka yanke masa bisa laifukan yaki da cin amanar kasa da taka rawa wajen tayar da kayar baya, dole ne tsohon shugaban na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Joseph Kabila, ya biya dalar Amurka biliyan 33 a matsayin diyya ga fararen hula a lardunan Kivu ta Arewa da ta Kudu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani