1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSiriya

Siriya: Martani kan kifar da gwamnati

Abdullahi Tanko Bala LM
December 9, 2024

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da martani kan halin da ake ciki a Siriya, bayan da 'yan tawaye suka hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad.

Siriya | Gwamnati | Bashar al-Assad | Faransa
Wasu al'ummar Siriya na tsallaen murnar kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a FaransaHoto: Bastien Ohier/Hans Lucas/AFP/Getty Images

Yadda 'yan tawaye a Siriya suka kifar da gwamnatin Bashar al-Assad ya shammaci kowa, kuma ya bayar da mamaki. 'Yan tawayen karkashin jagorancin Hayat Tahrir al-Sham sun kwace Damascus babban birnin kasar, bayan kaddamar da farmakin da ya sanya Shugaba Assad ya tsere zuwa Rasha ba tare da turjiya daga sojojin gwamnatinsa ba. Rasha ta tabbatar da cewa Assad da iyalansa sun isa birnin Moscow, kuma ta ba su mafaka kan dalilai na jin-kai. Kasashen duniya dai na ci gaba da yin martani kan halin da ake ciki a Siriyan, inda shugaban Amurka Joe Biden ya ce za su tuntubi dukkan kungiyoyin Siriyan domin samar da tafarkin shugabanci da ya zai banbamta da na Assad don dorewar kasar a matsayin mai cin-gashin kanta.

Karin Bayani: Sababbin hare-haren ta'addanci a Siriya

Fadar gwamnatin Chaina a Beijin a nata tsokacin ta ce, tana bi sau da kafa abin da ke faruwa a Siriyan tare da fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali zai dawo. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi a nasa bangaren ya ce, Tehran na fatan ci gaba da dangantakar aminci da abokantaka da Siriya. Ya ce Iran ta bude kafar tuntuba da 'yan tawayen, a kokarin kwantar da tashin hankali a tsakanin kasashen biyu. Ya kuma baiyana fargaba game da yiwuwar fadawar kasar cikin yakin basasa. Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce kasarsa wadda ta taimaka wa 'yan tawayen na Siriya, za ta taimaki kasar wajen shawo kan matsaloli da kuma hadin kanta tare da tabbatar da tsaro.

Bashar al-Assad ya yi bankwana da kujerar mulkiHoto: Mikhail Tereshchenko/TASS/dpa/picture alliance

Moscow babbar aminiyar Assad ta ce sojojin Rasha da ke Siriya suna cikin shirin ko-ta-kwana, sai dai ta ce 'yan tawayen sun tabbatar musu da tsaron sansanoninsu da ke kasar. Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga al'ummar Siriya na su yi amfani da wannan dama wajen samar da kyakkyawar makoma da zaman lafiya a kasar, bayan shekaru 14 na mummunan yaki. Wakilin musamman na majalisar a Siriya Geir Pedersen ya yi kira ga kungiyoyi masu dauke da makamai, su kare fararen hula da kuma tabbatar da tsaron hukumomin gwamnati.

Karin Bayani: Turnuku tsakanin Siriya da Turkiyya

Kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya su ma sun yi tsokaci, inda shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce kawo karshen mulkin Assad a Siriya abu ne mai kyau. Ya kara da cewa babban abin da ya kamata a mayar da hankali a kai cikin gaggawa shi ne, dawo da doka da oda a kasar. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ta bakin ministansa na wucin gadi mai kula da harkokin kasashen waje Jean-Noel Barrot ya ce, Faransa za ta goyi bayan kafa gwamnati cikin ruwan sanyi kuma za ta tura wakili na musamman nan da 'yan kwanaki masu zuwa. Ita ma kasar Saudiyya ta yi kiran kare Siriya daga wargajewa, tare da fadawa cikin rudani.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani