1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Martani kan kiran Amurka na neman a soke sharia

Nasir Salisu Zango SB
February 25, 2026

Wani sabon kira daga kwamitocin majalisar dokokin Amurka na neman a soke shariar Musulunci da dokokin hukunta masu sabo, ya bude sabon cece-kuce a tsakanin masana da sauran alummar Najeriya.

Birnin Kano na Najeriya na lalata barasa
Birnin Kano na Najeriya na lalata barasaHoto: AFP/AMINU ABUBAKAR

 

Dan majalisar Amurka Riley Moore ya gabatar da rahotan wasu kwmaitocin majalisar ga fadar White House, wanda karara rahotan ya kunshi shawarar neman a soke dokokin sharia da na batanci ko kuma sabo a Najeriya tare da wasu matakai kan tsrao da kariya gay an kasa.

Hangen masana

Wannan rahoto dai ya sake bude fagen cece-kuce, a Najeriya, wanda yawnacin masana ke sukar lamirin Amurka na yi wa Najeriya shiga sharo ba shanu. Barista Abba Hikima Fagge, lauya ne da ke faftukar kare hakkin dan adam ya ce, ko kadan Amurka ba ta da hurumin yiwa Nigeria katsalandan a harkokin ta na cikin gida.

Birnin Kano na NajeriyaHoto: Ben Curtis/AP Photo/dpa/picture alliance

Shi kuwa masanin siyasar kasa da kasa kuma farfdesa a jami'ar Bayero dake Kano Kamilu Sani Fagge, yace wannan shiga hanci da kudundune da Amurka kewa Nigeria yunkuri ne kawai na samun sansanin girke sojoji a Nigeria musamman ganin cewar Najeriya ta yi wasarere da hakkin ta na ‘yan tacciyar kasa.

Abin da hukumomi a Kano ke gani

Malam Ali Dan Abba kwamishina ne a hukumar sharia ta jihar Kano, ya bayyana cewar babu ruwan biri da gada tsakanin Amurka da shariar musulunci domin kowanne Allazi da nasa amanu

Birnin Kano na NajeriyaHoto: KOLA SULAIMON/AFP/Getty Images

Kan wannan batu na yiw akiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda Amurka ta sanya takunkumi ga wasu mutane ciki har da tsohon gwamnan Kano Dr Rabiu Musa Kwanwkaso, wanda aka girka shariar musulunci a kano zamanin mulkin sa, sai dai wani dan majalisar dokokin jihar Kano yayi kira ga majalisar da ta rubutawa shugaban kasa wasikar goyon baya ga kwankwason tare da barranta shi da duk wani batu na muzgunawa kiristoci

Yanzu haka dai ana cigaba da martini da fashin baki kan wannan batu wanda ke neman raba kan alumar kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani