1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin kotun duniya a kan kasar Isra'ila

Zainab Mohammed Abubakar MYA/SB/MA
January 26, 2024

Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta kada kuri'ar amincewa da umurtar Isra'ila ta dauki duk matakan dakatar da duk wani abu da ya shafi kisan ƙare dangi a yankin Zirin Gaza na Falasdinua, kuma aka fara mayar da martani.

Wajen Duniya duniya da ke kasar Netherlands
Wajen Duniya duniya da ke kasar NetherlandsHoto: Remko de Waal/ANP/AFP/Getty Images

Kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole ne Isra’ila ta hana kisan kiyashi a yakin da take yi da Hamas, sannan ta ba da damar kai agaji a Gaza, amma ta gaza yin kira da a kawo karshen fadan. Har ila yau,kotun ta ce dole ne Isra'ila ta dauki matakan gaggawa don tabbatar da samar da agajin jinkai da na yau da kullun da ake bukata cikin gaggawa a Zirin na Gaza.

Karin Baynai: 

Wajen Duniya duniya da ke kasar NetherlandsHoto: Piroschka van de Wouw/REUTERS

Kotun ta kasa da kasa ta kuma ce dole ne Isra'ila ta saukaka hanyopyin kai agajin jin kai cikin gaggawa ga Gaza, wadda ke fama da hare-haren bama-bamai da kuma kawanya tun bayan harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da hukuncin wanda ya bayyana da zama "abin takaici ne" yayin da mahukuntan Hamas na Gaza suka yaba da hukuncin kotun ta ICJ, kan cewar zai  taimaka wajen mayar da Isra'ila saniyar ware da kuma tona asirin laifukan da ta aikata a Gaza.

Wajen Duniya duniya da ke kasar NetherlandsHoto: Patrick Post/AP Photo/picture alliance

Sai dai a martaninsa ministan harkokin wajen Iran Hossein Amirabdollahian, ya yi kira ga hukumomin Isra'ila da su fuskanci shari'a bayan da kotun duniya ta umurci Isra'ila da ta dauki matakan hana aiwatar da kisan kare dangi a Gaza.

Ita ma Spain wacce ke daya daga cikin kasasahen Turai masu sukar farmakin da Isra'ila ke kai wa Hamas, ta yi maraba da hukuncin kotun kolin MDD na wannan Juma'a.