Martani kan komawar shugaban Sudan gida
June 16, 2015Kasar Amirka ta nuna rashin jin dadinta dangane da yadda aka kyale Shugaba Omar al-Bashir ya koma gida daga kasar Afirka ta Kudu inda ya halarci taron kungiyar Tarayyar Afirka, duk da sammacin da yake fuskanta daga kotun duniya mai hukunta masu manyan laifukan yaki ta duniya.
Sai dai mai-magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar bai fito fili ya soki yadda Afirka ta Kudu ta kyale Shugaba al-Bashir ya koma gida ba. Amma Amirka ta nuna takaicin yadda shugaban ya halarci taron.
Yayin da Shugaba al-Bashir ya samu gagarumar tarba lokacin da ya koma gida, masu mafutuka na kasar Afirka ta Kudu sun nuna takaicin yadda gwamnati ta kasa cika muradun kundin tsarin mulkin kasar, na bin umurnin kotun da ta hana shugaban na Sudan ficewa daga cikin kasar.