Najeriya: Kalubalen 'yan takarar shugaban kasa
May 30, 2022A Najeriya manyan jam'iyyun siyasa biyu na APC mai mulki da PDP ta ‘yan adawa na fuskanta takarar shugaban kasa a shekara mai zuwa, jam'iyyun da dukkaninsu ke da kalubale mai yawa, abin da ya sanya su fara rawar kafa tun daga wajen zaben fid da gwani da PDP ta kai ga kamalla nata.
Samun nasarar kai wa ga zama dan takarar neman shugabancin Najeriya da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi, ya sanya murna da doki ga dubban magoya bayansa, to sai dai kai wa ga wannan mataki ba sabon abu bane a gare shi, domin sau biyar yana takara ta neman shugabancin Najeriya farawa daga shekarar 1993 duka ba tare da ya samu nasara ba.
Kai wa ga wannan mataki a wannan karo, ya kasance cike da kalubale musamman yadda yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya suka dage a kan batun shugabanci da ma yadda zaben ya kasance. Dakta Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa a jami’ar Abuja ya bayyana kalubalen da yake hange ga jam'iyyar PDP.
‘’Ya ce, akwai maganganun da wasu suke yi musamman ‘yan kudancin kasar, a kan cewa bai kamata mulki ya koma arewa ba sai kudu, Atiku ya dade yana takara bai samu nasara ba, ya kamata ya tambayi kan shi me yasa baya samun nasara. Amma babban kalubale shi ne shi dan takarar jam'iyyar adawa ne, don haka zai yi takara ne da jam'iyya da ke mulki’’
Tuni dai jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shiga laluben mafita. Duka jam'iyyun biyu sun shiga wasan buya a kokarin lalubo da dubarar yadda za su tunkari zaben da za’a yi a shekara mai zuwa. Mallam Bashir Baba mai sharhi ne a fanin al’amuran yau da kullum a Najeriyar, ya baiyana fahimtarsa a kan kalubalen da ake ciki.
Dukkanin jam'iyyun na da kalubale na cikin gida da na waje a kan zaben da ke daukan hankali sosai, alal misali, ko bayan sanar da zaben Atiku Abubakar, akwai ‘yan takara irin su gwamna jihar Rivers Nyesom Wike da Anyim Pious Anyim da ba su hau dandalin da ya yi jawabi ba a Abuja bayan nasarar.
‘Yan Najeriya sun bude idannunsu a kan babban zaben da ake sa ran sauyin da aka samu a dokar zabe zai taimaka kyautata tsarinsa, domin duk da zargi na amfani da kudi wajen fitar da ‘yan takara amma dokar ta tilasta yin zabe da kawar da karfa-karfa iri ta jam'iyya abin da ya sanya manyan ‘yan takara shan kaye a zaben fidda gwani.