1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tinubu na samun martani kan neman mulkin Najeriya

January 11, 2022

Bayan aiyana burinsa na takara bisa shugaban Najeriya, jagoran APC kuma tsohon gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu na neman hargitsa lamura cikin fagen siyasar kasar da ke ta mai da martani.

Najeriya, Abuja, Muhammadu Buhari, Bola Ahmed Tinubu tsohon gwamnan Legas
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da Bola Ahmed Tinubu tsohon gwamnan jihar LegasHoto: Official-State House Abuja Nigeria

 

Ya dai dauki lokaci yana yiwa kansa kirari na jagaba na siyasar jam'iyyar APC mai mulki, kuma yai dimbi na magoya baya da masu takama da kiyyayar gado, yai kuma nasarar nadawa da sauke da dama a mukamai na siyasa ta kasar. To sai dai kuma daga dukkan alamu kokarin Bola Ahmed Tinubu na dandana mulkin tarrayar Najeriya dai na dauka ta hankali a tsakani na abokan taku da maabokai na adawa cikin kasar a halin yanzu.

Dan shekaru 69 kuma tsohon jagoran NADECO mai fafutukar kare hakkin Yarabawa, Tinubu dai ya taka rawa cikin harkokin siyasa ta kasar tun daga jamhuriya ta biyu.

Shugaba Muhammadu Buhari da Bola TinubuHoto: Official-State House Abuja Nigeria

Kuma wata hadaka a tsakaninsa da shugaban dake kan mulki ko bayan wasu jam'iyyu guda biyu ne dai ake ta'allakawa da kai karshen mulkin PDP na shekaru dai dai har 16. To sai dai kuma aiyyana takarar tasa na neman yamutsa hazo cikin fagen siyasar tarrayar najeriyar da ke kara duhu yanzu.

Kaso 60 cikin 100 na 'yan zaben a shekarar badin dai na a tsakanin shekaru 18-40, adadin da ya kai miliyan 84 ya kuma ninka kusan kaso hudu na yawan kuri'ar da ta kai Shugaba Muhammadu Buhari kan gadon mulki na kasar a shekarar 2019.