1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan sabon shugaban PDP

January 19, 2011

Ƙasa da watanni huɗu kafin zaɓen gama gari da zai gudana a Najeriya, sai gashi jam'iyar PDP ta samu sabon shugaba daga arewa, hakan ya jawo martani da yawa.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.Hoto: AP

Masana da masharhanta a Tarayyar Najeriya sun fara tofa albarkacin bakin su bisa sauyin shugabanci a jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, inda mafiya yawan su suka bayyana cewa matsalolin da suka yiwa jam'iyar katutu, su ne suka fara bayyana. Wasu kuwa na ganin cewa wata dabarace ta mai da shugabancin jam'iyar daga kudu zuwa arewa, ganin yanzu shugaba Jonathan wanda ya fito daga kudu shine zai tsayawa jam'iyar takaran shugabanci. Abinda kan iya sauya tunanin 'yan arewacin ƙasar.

Kuna iya sauraron sauti a rahoton da Wakilin mu a Gombe Amin Sulaiman Mohammad ya aiko mana.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal