1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan sake zaben Netanyahu

Mahmud Yaya Azare
March 3, 2020

Duk da nasarar sake lashe zabe da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyehu ya yi, jam'iyyarsa ba ta sami rinjayen da zai ba shi damar kafa gwamnati ba, lamarin da ya jawo martani daga 'yan kasar da ma kuma Falasdinawa.

Parlamentswahl in Israel Sieger Likud Netanjahu
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Bality

Netanyahu wanda ke zama firaministan Isra'ila na farko da aka zaba har sau uku a jere duk da fuskantar tuhumar cin hanci da ake yi masa wanda kuma a yayin alkawuran zabensa ya sha alwashin kwace iko da yankunan falalsdinawa dake Yamma da Gabar kogin Jodan, ya siffanta nasarar da jam'yyarsa ta samu da cewa gagarumar nasara ce ga kasar Isra'ila.

"Wannan ita ce nasara mafi dadi da muka taba samu a tarihinmu saboda nasara ce da ta saba wa dukkan hasashe. 'Yan adawa na ta ikrarin cewa, Netanyahu sai buzunsa, amma albarkacin goyan bayanku, sai ga shin Netanyahu ya gagaresu. Alal hakika kun mayar mana da lemon tsami ya zama na zaki."

Netanyahu da 'yan jam'iyarsa ta LikudHoto: AFP/J. Guez

To sai dai duk da wannan nasarar da yayi, jam'iyyarsa ta Likud na fuskantar kalubalen kafa gwamnati, bayan da abokin hamayyarsa Benny Gantz da ya zo na biyu da kujeru 33 ya ce zai ci gaba da zama dan adawa.

"Na fahimmci irin takaicin da muka tashi da shi na rashin samun sakamakon da muke fatan samu. Abin da ya fi bamu takaici shi ne, idan har wannan sakamakon zaben ya tabbata a hukumance, to Isra'ila za ta koma gidan jiya kenan, wato karkashin jagoranci mabarnatan shugabannin da ba za mu ta ba yadda mu shiga kawancen hada gwamnati da su ba."

Wasu magoya bayan NetanyahuHoto: AFP/J. Guez

Duk da fuskantar shari'ar da ya ke, da kuma zarginsa da zakewa wajen dogaro da Amirka wajen cimma muradun Isra'ila da ake ganin za su iya sauyawa idan aka samu wasu sabin shugabanni a Amurka, sai dai galibin 'yan kasar da suka zabeshi da kaso kusan 59 cikin dari, na kallonsa a matsayin gwarzonsu a lokacin yaki da kuma zaman lafiya.

To sai dai a hannu guda, Falalsdinawa su na daukar nasarar Netanyahu a matsayin wata sabuwar annobar da ba a san karshenta ba.