Martani kan shirin Tinubu a jihar Plateau
April 3, 2026
Al'ummomin jihar Plateau na martani kan ziyarar da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai jihar don jajenta musu game da halin tashe tashen hankula da ake fama da su, inda kuma ya sha alwashin cewar gwamnatinsa za ta kawo karshen matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Yayin ziyarar dai Shugaba Tinubu ya sanar da cewar za a sanya kyamarori kimanin dubu biyar, don a rika gano mutanen da ke kai hare-hare tsakanin birane da ma yankunan kananan hukumomin jihar da ake fama da matsalolin tsaro.
ganawa lokacin ziyarar
Yayin ziyarar shugaban ya gana ne da masu ruwa da tsaki daga bangarorin al'umma daban-daban inda ma ya tabbatar da cewar gwamnatinsa za ta kawo karshen duk matsalolin tsaro da ake fama da su inda yake cewar za a kafa sabbin kyamarori na zamani fiye da 5,000, da za su rika taimakon jami'an tsaro.
To sai dai a gefe guda baya ga matsalolin tsaro da ke aukuwa a cikin biranen jihar mazauna yankunan karkara na fama da hare-haren 'yan bindiga wanda kan yi sanadiyar rasa rayukan mutane.
Wasu daga cikin shugabanin al'ummomin jihar Plateau na korafi ne kan yadda suka ce shugaban kasar bai shigo gari ba a ziyarar don ganewa idonsa yanayi da jihar ke ciki, kasancewar ya gana ne da wasu shugabanni kalilan a harabar filin saukan jiragen sama na jos.
Zuwa yanzu ma dai rundunar sojin Najeriya ta tura karin dakaru 850, zuwa jihar a kokarin magance matsalolin tsaro da jihar ke fama da su.