Cece-kuce kan soke galibin jam'iyyun siyasa na Najeriya
February 7, 2020Wannan mataki da ya katse hanzarin jamiyyun 74 na Najeriya da a ytanzu suka shiga kundin tarihi bisda matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta dauka, bisa abinda ta kira rashin tabuka wani abin a zo a gani a zaben da aka yi a 2019. Duk da koke da ake yi a kan lamarin hukumar zaben ta ce abin da ta yi yana bisa doka.
Tuni dai jam'iyyun da abin ya shafa suka harzuka, nuna fushi da ma maida murtani cewa soke jamiyyun nasu bai dace ba, kuma suna da ja a kan dalilan da hukumar zaben Najeriyar ta bayar.
Jam'iyyun siyasa a Najeriya dai sun kama hanyar zama taron yuyu-yuyu, inda a zahiri wadanda aka sani ba su wuce guda biyar ba. Dr Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da ke Abuja ya bayyana hasashensa ga wannan mataki na soke jamiyyun 74 a Najeriya.
Masaharahanta na bayyana cewa muddin ba wani tsari aka sauya ba haka za a ci gaba da yi wa sabbin jam'iyyu rijista bayan an gama zabe a soke wasu, saboda yadda aka mayar da siyasar a matsayin sana'ar da ake zuba jari a cikin don cin riba ba wai bisa akida ba.