Martani kan takarar Angela Merkel
November 21, 2016Fitowa fili da Shugabar gwamnati Angela Merkel ta yi a ranar Lahadi ta bayyana cewar za ta sake neman wani wa'adin mulki wanda shi ne zai kasance irinsa na hudu da shugabar 'yar shekaru 62 da haihuwa za ta yi ya sanya masana harkokin siyasa a nan Jamus yin nazari tare ma da bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta kan wannan batu. Masu adawa da shugabar ta gwamnati da ma jam'iyyarta ta CDU na ganin lokaci ya yi da Merkel za ta bar gadon mulki domin a samu sauyi shugabanci da ma manufofin da suke daban da irin wanda ta shafe wa'adi ukun da ta yi ta na aiwatarwa.
To sai dai masana harkokin siyasa irinsu Frank Decker na Jami'ar Bonn na ganin tun da ba wani kayyadajen wa'adin mulki da kasar ke da shi shugabar na iya cigaba muddin dai al'umma da ma jam'iyyarta ta CDU ta ba ta damar cigaba da jagorantar kasar.
''Masu zabe sun gamsu da irin kamun ludayinta. Idan da jam'iyyarta ta CDU za ta ce irin yadda ta ke tafiyar da mulki ya saba da yadda ake muradi to fa ba za ta ci zabe ba, ka ga wannan na nuna cewar tun daga cikin gida za a iya taka mata birki sai dai ya zuwa yanzu hakan ba ta kasance ba tukunna ba.''
Wadannan kalamai na Decker dai sun saba da yadda jam'iyyun da ke adawa a nan Jamus ke kallon lamarin domin kuwa da damarsu na ganin lokaci ya yi da Merkel za ta yi bankwana da shugabanci domin a cewarsu salon mulkinta ba abu ne da ya gamsar da yawa-yawansu ba musamman ma idan ana magana batun rungumar 'yan gudun hijira wadda shugabar ta yi.
A shafukan sada zumunci na Facebook da ma sauran kafofi na cigaba da tofa albarkacin bakunansu kan batun. Alal misali a shafinmu na Facebook na DW Hausa, Isa Lawal Girgir na ganin ko kusa bai kyautu Merkel ta sake takara ba don kuwa hakan na kama da makalewa kan gadon mulki da shugabannin Afirka ke yi wanda kasashen Yammaci ke adawa da shi.
To sai da wasu da dama ciki kuwa har da Isiyaku Hamza Gogori na ganin matakin da shugabar gwamnatin Jamus din ta dauka na sake neman wani sabon wa'adin mulki ya yi daidai kasancewar kundin tsarin mulkin Jamus din ba kayyade yawan shekarun da shugaban gwamnati zai yi kan gadon mulki ba.