1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Zirin Gaza: Ko an kawo karshen yaki?

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim LM
January 16, 2025

Kasashen duniya na ci gaba da bayyana jin dadinsu da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas, domin dakatar da yakin Zirin Gaza, wanda aka shafe tsawon watanni 15 ana gwabzawa.

Falasdinu | Deir al-Balah | Murna | Tsagaita Wuta | 2025 | Yaki | Isra'ila | Hamas
Tsallen murna bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Hamas ta Isra'ilaHoto: Ashraf/UPI PHoto/IMAGO

Yakin na yankin Zirin Gaza na Falasdinu dai, ya yi sanadiyyar mutuwar dubban Falasdinawa musamman ma mata da kananan yara. Haka ma daruruwan Isra'ilawa ne suka halaka, yayin da har yanzu kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai a Zirin Gazan da ke gwabza yaki da Isra'ilan ke garkuwa da wasu Isra'ilawa da suka kama a yayin harin ranar bakwai ga watan Oktoban 2023. Tuni dai shugabannin Kasashen Yamma, ke mayar da martani game da wannan sulhu mai cike da tarihi da aka cimma. An dai kasafta tsarin aiwatar da yarjejeniyar zuwa rukuni uku, kuma za ta fara aiki a ranar Lahadi mai zuwa.

Karin Bayani: Hezbollah da Isra'ila sun cimma yarjejeniya

Firaministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani ne, ya sanar da batun cimma yarjejeniyar a birnin Doha. Qatar din ce ta dauki dawainiyar karbar bakuncin zaman lalubo hanyar sulhuntawar ta tsawon lokaci, a karkashin jagorancin Amurka da Masar. Hamas dai ta amince da sakin wasu Isra'ilawa da ta yi garkuwa da su, yayin da Isra'ila za ta sako daruruwan Falasdinawan da ke garkame a hannunta tare da bai wa Falasdinawan Gaza damar komawa muhallansu da aka ragargaza. A hannu guda akwai tarin kayan agajin jin kai da za a shigarwa Falasdinawan, domin sake murmurewa daga bala'in yunwa da suka tsinci kansu a ciki sakamakon yakin.

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

02:06

This browser does not support the video element.

Shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya nanata cewa yarjejeniyar zaman lafiyar za ta ci gaba da wanzuwa matukar bangarorin biyu suka ci gaba da amincewa da zama kan teburin sulhu, domin martaba sharuddan da aka gindaya. A cewarsa shi da magajinsa mai jiran gado Donald Trump na da ra'ayi guda, na ganin an tabbatar da zaman lafiya a yankin Zirin Gaza. Ministar harkokin kasashen ketare ta Jamus Annalena Baerbock na daga wadanda wannan daidaitawa ta farantawa rai, ko da yake tana da hanzari kan amincewar Isra'ila a kai. A cewarta tsawon kwanaki 470 iyaye suka kasance cikin fargabar ko wane hali 'yayansu ke ciki, sakamakon garkuwar da Hamas ta yi da su kuma akwai kananan yara a cikinsu har ma da Jamusawa.

Karin Bayani: Antony Blinken na ziyara a Yankin Gabas ta Tsakiya

Baerbock ta kara da cewa akwai rahotanni da ke nuna tabarbarewar halin jin kai da al'ummar Gaza ke ciki, yanzu ko da wahalar ta kawo karshe bai kamata gwiwowi su yi sanyi ba har sai haka ta cimma ruwa. Birtaniya ma ba a barta a baya ba wajen maraba da wannan ci gaba da aka samu, inda sakataren harkokin wajenta David Lammy ke ayyana lamarin a matsayin cikar wani gagrumin buri. Yanzu dai ana dakon jin ra'ayin gwamnatin Isra'ila wadda ke jan kafa wajen fitar da matsayarta a kai, sakamakon bullar rahotoanni da ke cewa tana nuna tirjiya kan wasu bukatu gabanin karkare komai. A hannu guda Amurka na kai gwauro da mari, domin tabbatar da nasara a kai.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani