1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yan Filato na martani kan Dariye

Abdullahi Maidawa Kurgwi
August 12, 2022

Jama'ar Filato na bayyana ra'ayoyi mabanbanta dangane da afuwar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi wa tsohon gwamnan jihar Joshua Dariye bayan kotu ta daure shi kan laifin sace dukiyar jihar.

Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Tun  dai a ranar 14th, ga watan Afrilun wannan shekarar ce majalisar koli ta tarayyar Najeriya ta yi afuwa ga wasu yan Najeriya 159, ciki har da tsoffin gwamnoni biyu, Jolly  Nyame na jihar Taraba da Joshua Dariye na jihar Filato. To sai dai tuni wasu 'yan Najeriyar  suka soma nuna shakku  ga ikirarin gwamnatin shugaba Buhari na yaki  da cin hanci da rashawa

A   jihar Filato  dai  tun bayan fitowar Dariye daga gidan yarin kuje, wasu jama'ar jihar musaman 'yan asalin karamar hukumar Bokkos  maihaifar Dariye, suke ta bukukuwan murna.

To amma a cewar Madam Ladi sakin Dariye rashin adalci ne ga duk 'yan Najeriya dake tsare da suka aikata kananan laifuka wadanda ake cigaba da tsare su.

Wasu al'ummar jihar Filato na gani cewar sakin tsohon gwamnan bai kamata ba, don kuwa a lokacin gwamnatinsa ne  jihar Filato ta fuskanci  mummunan tashe tashen hankula shekarun baya,  wasu kuwa cewa suke sakin Joshua Dariye lamari ne da ya chanchanta sakamakon halin da ya shiga yayin da kuma wasu ke daganta sakin tsoffin gwamnonin biyu kan lamari na siyasa tsantsa.