Martanin al'ummar Najeriya bayan mutuwar Abubakar Shekau
September 25, 2014Da dama dai wannan sanarwa ba ta zo musu da mamaki ba musamman ganin dama an ɗauki kwanaki ana yaɗa hoton mutumin da ake cewar shi ne Abubakar Shekau jagoran Kungiyar Boko Haram.
Sama da 'yan Ƙungiyar Boko Haram 260 suka miƙa wuya ga sojojin Najeriya
Ga misali a garin Maidugri fadar gwamnatin jihar Borno an yaɗa wannan hoto tsakanin wayoyin mazauna garin tare da hotunan wasu gawarwaki da ake ce na ‘yan ƙungiyar ne da aka hallaka a fafatawar Konduga.Bayan bayyana kashe mutumin da Sojojin ke cewa Jagoran masu gwagwarmayar ne, rundunar tsaron ta kuma bayyana cewar ta hallaka wasu ‘yan ƙungiyar da dama wasu darurruwa kuma sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga sojojin Najeriya.
Ra'ayoyin jama'a dangane da mutuwar Abubakar Shekau
Wannan ya sa wasu al'ummar sassan jihar Borno bayyana farin ciki saboda suna ganin an fara kawo ƙarshen wannan yaƙi da ya lamushe rayukan dubban al'umma tare da korar wasu da dama daga matsugunansu. Ga abin da wani mazaunin Maidguri ke cewa ta wayar tarho kan yanayin da garin yake ciki bayan tabbacin da Sojojin suka bayar
''Maidugri ana cikin halin na jin daɗi na murna duk wanda ka gani yana murmushi yana murna ba kamar yadda aka saba gani ba a baya,sakamkon cewar rundunar sojoji ta ce Boko Haram suna ajiye kayan faɗa suna cewar ba yaƙi''
Sauran al'ummomin yankin Arewa maso gabshin Najeriya kuma na bayyana ra'ayoyinsu da ke nuna shakku, yayin da wasu ke cewar kashe Shekau ba shi ne masalha ba, dole sai an nemo waɗanda ake zargi da hannun wajen tallafa wa ƙungiyar.