Martanin Burtaniya kan harin Isra'ila a Siriya
May 5, 2013Mr. Hague ya ambata hakan ne a wannan Lahadin inda ya kara da cewar ya kyautu a ce an janye takunkumin nan na makamai da aka kakabawa 'yan tawayen Siriya wanda ke rajin kawar da shugaba Assad daga gadon mulki.
Yayin da sakataren na harkokin wajen Burtaniya ke wadannan kalamai, a hannu guda Iran kira ta yi da a juyawa Isra'ila baya sakamakon harin da ta kai wa Siriya inda ta ce a shirye ta ke da ta tallafawa dakarun gwamnatin Siriya da horo irin na dabarun yaki.
Da sanyin safiyar yau ne dai jiragen yakin Isra'ila su ka kai jerin hare-hare kan wata cibiya ta bincike kimiyya da harkokin tsaro ta kasar ta Siriya, lamarin da ya sanya wajen yin dameji kamar yadda wanda su ka shaida harin su ka bayyana wa manema labarai.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru awal