1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan kisan mutane 12 a Faransa

Suleiman BabayoJanuary 7, 2015

Kasashen duniya ciki har da sa'udiyya na ci gaba da yin tir da harin ta'addancin a cibiyar mujallar Charlie Hebdo da ya hallaka mutane 12 a Paris na kasar Faransa.

Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Jami'an kasar Faransa sun tabbatar da mutuwar mutane 12 sakamakon harin kan wani ofishin wata mujalla mai fitowa mako-mako, wadda ta yi fice wajen zanen barkwanji, cikin wadanda suka hallaka akwai 'yan sanda biyu. Sannan akwai mutane hudu da suka samu raunika. Editan mujallar da 'yan jarida uku, da suka kasance gwanayen zabe da suka fice a Faransa suna cikin wadanda suka mutu.

Shugaba Francois Hollande wanda ya ziyarci wajen da lamarin ya faru, ya ce babu makawa wannan hari na ta'adaci ne da aka kai wa mujallar ta Charlie Hebdo. Tuni Shugaba Hollande ya kira taron gaggawa, domin duba yanayin tsaro, dama an karfafa matakan tsaro a wuraren taruwan jama'a.

Shugabannin siyasa da na addini a kasashen duniya sun yi tir da harin. Firaministan Birtaniya David Cameron ya yi kakkausar suka kan hari da aka kai na Faransa. Kasar Saudiya da addinin Islama ya samo asali na cikin wadanda suka tir da harin kan ofishin mujallar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe