1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin EU ga hari kan coci a Masar

January 2, 2011

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa Kristoci a Masar

'Yan sandan kwantar da tarzoma a inda aka kai harin.Hoto: AP

Ƙungiyar Tarayyar Turai, EU ta yi Allah wadai da kakkausan harshe da harin da aka kai a jiya Asabar a wajen wani coci a ƙasar Masar. Mutane 21 suka rasa rayukansu a cikin wannan hari wasu kuma 80 sun jikata. Kantomar Ƙungiyar Tarayyar Turai kan manufofin ƙetare, Catherine Ashton ta ce babu hujja game da wannan hari wanda shine na baya-bayan nan a cikin jerin hare haren da ake kai wa Kristoci a faɗin Gabas ta Tsakiya. Shugaban cocin Katolika na duniya, Papa Roma Benedict na 16 shi kuma ya yi tofin Allah tsine game da wannan hari, ya kuma yi kira ga Kristoci da cewa kada su razana bisa wariyar da ake nuna musu. Shugaban Masar, Hosni Mubarak ya ce 'yan ta'adda daga ƙasashen ƙetare ne suka ƙaddamar da harin domin jefa ƙasar a cikin ruɗani.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Mohammad Nasiru Awal