Najeriya: Martanin Fulani kan hana yawo
February 1, 2021Rikicin makiyaya da manoman Tarayyar Najeriyar dai, na neman ganin bayan tsohuwar al'adar kiwo. Al'adar kiwon dai na zaman yawo da dabbobbi a burtali da sauran labi-labi, daga sashen arewacin kasar zuwa na kudancinta. Al'adar kuma da ke dada daukar hankali cikin kasar da ke fama da rikicin rashin tsaro a halin yanzu. An dai kai ga sanar da jerin tsare-tsaren da suka hada da shirin sake tsugunar da masu sana'ar kiwon na RUGA, an kuma ce ana shirin kashe dubban miliyoyin Naira da nufin kai wa ga samar da wuraren kiwo da ma makarantu ga Fulanin da ke cikin sana'ar kiwon. Sai dai an gaza kai wa ga shawon rikicin da ke dada sauyin launi da salo cikin kasar a halin yanzu.
Karin Bayani:Cimma yarjejeniyar sulhu da makiyaya
To sai dai gwamnan jihar Kano daya kuma a cikin jagorori na Fulani a kasar Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce, ana bukatar kafa dokar haramta daukar shanun daga sashen arewacin Najeriyar zuwa kudanci da sunan kiwo, wanda wasu ke yi wa kallon abin da ya haddasa rashin tsaron da ke zaman ruwan dare game duniyar kasar. Ganduje dai ya ce ana bukatar haramta safarar shanunn ko dai a cikin manyan motoci ko kuma a kasa, daga sashen arewacin kasar zuwa ragowar sassa, in har ana neman hanyar kai karshen tashin hankalin makiyaya da manoma.
Kalaman na Ganduje dai ga dukkan alamu ba su dadada ran kungiyoyin Fulanin kasar ba, wadanda ke ganin an yi su ne da biyu. Alhaji Usman Baba dai na zaman sakataren kungiyar Fulanin Najeriyar ta Miyetti Allah ta kasa, wanda kuma ya ce ba hujjar haramta kiwo a kasar ba tare da ingantaccen tsari ga masu kiwon na zama wuri guda domin kyautata harkar ba. Najeriyar dai na da yawan shannun da ya kai kusan miliyan 20 da kuma mafi yawansu ke kai kawo a tsakanin sassan arewacin kasar zuwa na Kudu, a cikin neman ruwa da wurin hakki.
Karin Bayani:Mayar wa Fulani burtalai a fadin Jigawa
Kuma a fadar Mohammad Dodo Oroji wani da ke zaman mai sana'ar kiwon a Najeriyar, tana iya samun ci gaba mai nisa in har aka koma ya zuwa sarrafa naman shannun a sashen arewacin kasar. Kokari na rataye kare a laifin kura ko kuma kokari na zamanantar da sana'ar kiwon dai, Isa Tafida Mafindi ya kashe daruruwan miliyoyin Naira a kokarin kafa mahauta ta zamani a Abuja fadar gwamnatin kasar, kuma a fadarsa Najeriyar na da babbar dama a cikin rikicin makiyaya da manoman da ke iya kai kasar zuwa ga ci-gaba. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kaya wa a cikin kasar da ke da dukiya ba adadi, amma kuma ke ninkaya a cikin tsanani na talauci.