Martanin gabas ta tsakiya kan daftarin MDD
August 6, 2006Shugabanin yankin gabas ta tsakiya na cigaba da mai martani a game da daftarin kudirin Majalisar dinkin duniya da nufin dakatar da Artabun da ake yi tsakanin Israila da dakarun Hizbullah. Bayan tsawon kwanaki ana ta musayar raáyi ta fuskar diplomasiya, a karshe Faransa da Amurka sun cimma yarjejeniya a kan daftarin kudirin a jiya. Daftarin dai ya bukaci dakatar da fadan baki daya, amma bai baiyana jadawalin lokaci na kawo karshen fadan ba. Hakan nan kuma ya bukaci kafa sojin gamaiyar kasa da kasa karkashin Majalisar dinkin duniya wadanda zaá tura zuwa kudancin Lebanon domin tabbatar da zaman lafiya. P/M Lebanon Fuad Siniora ya yi kakkausar suka ga daftarin wanda ya baiyana da cewa bai gamsar ba. A hannu guda kuma kakakin gwamnatin Israila Avi Pazner yace Israila zata cigaba da farmakin da take yi har ya zuwa lokacin da sojojin gamaiyar kasa da kasan za su isa kasar Lebanon.