Martanin Isra'ila game da hana kai agjin Gaza
June 30, 2011Ministan harkokin wajen Isra'ila Avigdor Lieberman ya yi kira ga 'yan fafutuka da ke shirin kai taimako zuwa zirin Gaza da su guje wa jefa yankin gabas ta tsakiya cikin wani sabon rikicin siyasa. Babban jami'in gwamnatin bani yahudu ya furta wannan kalaman ne domin kare gwamnatinsa dangane da zargin da ake yi mata na kawo cikas a karo na biyu ga ayarin jiragen ruwa da ke shirin kai agaji a yankin palesɗinuwa da isra'ilan ta killace.
A kwanakin baya dai, sojojin kundubalan Isra'ila sun yi wa jiragen masu fafutukar dirar miƙiya a lokacin da suka nufi zirin Gaza a inda suka kashe mutane da dama. Masu fafutukar sun ce a wannan alhamis, an lalata wani ɓangare na jirgin ruwansu a lokacin da suka ya da zango a mashigir ruwan Göcek na ƙasar Turkiya. Yayin da a ɗaya hannu kayan agajin da ke shake a jirgin ruwan da ke tsaye a ƙasar Girka suka fara lalacewa sakamakon rashin samun izinin shiga zirin Gaza.
A Baya dai, Isra'ila ta nunar da cewar ba za ta ƙyalle ayarin jiragen ruwan da suka ƙunshi mutane 200 da suka fito daga ƙasashe 22 su isa zirin na Gaza ba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Ahmed Tijjani Lawal