Martanin Jamus kan tura sojojin Amirka zuwa Afghanistan
August 23, 2017Ko da ya ke shugabar gwamnatin Jamus ba ta yi wani dogon jawabi ba kan shirin na Amirka, yayin da ta ke yin wata tattaunawa da wata mujallar sojan Jamus Bundeswehr, ta yi kalaman da ke zama abin jujuyawa a zukata, watau su dai suna matsayarsu, kuma shirye suke su ba da tasu gudunmawa kan yaki da ta'addanci tsakanin kasa da kasa. Shi kuwa Trump ya bayyana cewar yana da kwarin gwiwa na ganin daga wannan lokaci su kai farmaki ga makiyansu su kawar da IS su murkushe Al Qaida da taka birki ga Taliban mai kokarin kwace Afghanistan.
''Za mu tambayi kawayenmu na kungiyar NATO da sauran kawayenmu na sauran sassa na duniya su tallafa wa sabon yunkurinmu da karin soja da kudade, muna da karfin gwiwa za su yi.''
Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta jam'iyyar CDU jam'iyyar shugabar gwamnatin Jamus, a ranar Talata a yayin ziyararta a sansanin ba da horon sojan ruwa a arewacin Jamus ta bayyana cewar matakin da Amirka ta dauka na kara yawan sojanta a Afghanistan da cewa abu ne mai kyau, inda ta ce dama tuni Berlin ta kara yawan nata sojan, yayin da wasu kasashe suka janye nasu, ta ce hakan ya yi kyau da Amirka ta zo da mataki da ya sabawa na lokutan yakin neman zabe da Trump ke cewar ba za su ba da karin soja ba.