Martanin kasashe da kungiyoyin addinai kan harin Paris
January 8, 2015![Ukraine Botschaft Frankreich Kiew Anteilnahme Charlie Hebdo](https://static.dw.com/image/18177083_800.webp)
Talla
Mujallar dai ta taba wallafa zanen batanci wa Annabi Muhammad. Yanzu haka dai shugabannin kasashen duniya da dama sun yi Allah wadai da wannan harin.
A yanzu haka dai yan sandan kasar na ci gaba da binciken mutanen da suka kai hari, da shekarunsu yake 18 da 32 da 34.
Tun a ranar Larabarce dai aka fara gangami a biranen Turai da dama, domin nuna alhini kan harin na kasar Faransa. Dubban jama'a sun taru a biranen London, Berlin, Brussels, da makamantansu domin tunawa da wadanda suka mutu a harin na Charlie Hebdo.