Martanin kasashen duniya kan rikicin Isra'ila
May 12, 2021Tun daga ranar Litinin din data gabata ne dai dakarun Isra'ila suka kaddamar da hari a zirin Gaza, yayin da mayakan Falasdinu suma suka yi martani da harba rokoki sama da dubu daya, lamarin da ke zama mafi muni a cikin shekaru 7.
Da yake martanin Shugaba Vladmiri Putin na kasar Rasha ya bukaci bangarorin biyu da su mayar da wukakensu cikin kube yayin zantarwarsa da takwaransa na Turkiyya Racep Tayyip Erdogan wanda ya ce akwai bukatar a koyawa Isra'ila darasi.
Firanministan Birtaniya Boris Johson ya bukaci Isra'ilawa da Falasdinawan da su nuna halin dattako ta hanyar sassanta tsakaninsu.
Ita kuwa Jamus suka ta yi da kakkausar murya ga hare-haren rokoki daga zirin Gaza zuwa biranen Isra'ila, a don haka ta ce Isra'ila na da damar kare kanta. Sai dai kuma Amirka ta ce Isra'ilar bata da wannan damar saboda abin takaici ne ci gaba da samun adadin fararen hula da ke rasa rayukansu.
Kwamittin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na shirin yin taron gaggawa don lalubo bakin zaren matsalar.