Martanin Libiya kan zargin Sarkozy
March 22, 2018Tsohon shugaban na Faransa Sarkozy ne dai kan gaba wajen marawa yan tawayen Libiya baya, da tura jiragen yaki don kai hare-haren da suka kai ga halaka Kanal Gaddafi, abun da Masharhanta kewa kallon butulci, koma ace kokarin bad da sawun daya daga cikin badakalolin kudade da ya sabayi da shuwagabannin Afirka.
Kodayake, kamar yadda Qazzaful dam, dan Baffan kanal Gaddafin, shugaban ofishin siyasar harkokin waje a lokacinsa ke fadi, Kanal Gaddafin ya bawa Sarkozy Yuro miliyan hamsin din ne, don kishin Tarayyar Afirka:
"Gaddafi ya bawa Sarkozy tallafi ne, domin ya tabbatar da cewa, ba wanda ke gaba da kafuwar Tarayyar Afirka tamkar Faransa, wacce ta mayar da kasashen dataiwa mulkin mallaka shanun tatsa, ta kuma ci gaba da tirsasa musu al,adarta da yarenta ,don haka,a gaskiya wannnan tallafin maksudinsa, shine,kar Sarksy yayi adawa ko yai kafar ungulu a burin Kanal Gaddafi na ganin an samu kafuwar Tarayyar Afurka.”
Shi kuwa dan Kanal Gaddafin, Saiful Islam, wanda bayan ya samu 'yanci ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar ta Libiya da ake shirin yi kafin karshen shekara, nuna aniyarsa yayi tab a da shaida kan badakalar da ake tuhumar Sarkozyn da ita.
"Dole da farko Zarkozy ya dawowa da al,ummar Libiya kudaden tallafin da suka bashi, don butulci da cin amanar da yayi musu. A shirye nake in bada shaida kan kudaden da Libiya ta bashi, ina da dukkanin takkaduntura kudi da sunayen bankunan da aka tura mar kudin."
Shi kuwa Tahir Warfally, mai fafutukar kare hakkin bil adama a kasar ta Libiya cewa yayi, laifin da suke tuhumar Gaddafi ya fi gaban laifin badakalar kudade.
"Hukunta Sarkozi bai kamata ya takaita kan badakalar kudade ba, kamata yayi a fara tuhumar wargaza Libiya da yayi, da kuma diyyar jinin dubban mutane day a kashe, kan banda mayar da illahirin yankunanmu suka zama dandalin tashe tashen hankula da yake yake, bayan ya samemu muna zaune lami lafiyana".
Batun kwararar bakin haure zuwa Turai ma dai, laifi ne Ahmad Nusairi,wani dan majalisar Libiya , yace ya wajaba a tuhumi Sartkozin kansa.
"Sarkozy ne ummulhaba'isin wargaza Libiya, da yaduwar ta'addanci a cikinta, gami da rugurguza rundunar soji da jami,an tsaron dake kare iyakoki.Ba don hare harensa ba, bat a yadda za a samu kwararar bakin haure ta cikin kasashenmu."
Dr Ateef Haujah, malamin kimiyar siyasa, yace Yan Afurka suna yaudarar kansu,kadan har sukai zatan cewa,kasashen Yamma zasu goyi bayansu wajen yin dimokiradiya ta hakika,koma yin juyin juya halin da zai tabbatar musu da rayuwa mafi inganci