1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Pakistan game da bin Laden

May 3, 2011

Bayan sanarwar kisan shugaban ƙungiyar al-Qa'ida Osama bin Laden, jami'ai a Amirka na baiyana al'ajabi yadda ya zauna a Pakistan ba tare da sanin mahukuntan ƙasar ba

Shugaban kasar Pakistan Asif Ali ZardariHoto: picture-alliance/ dpa

Shugaban Pakistn Asif Ali Zardari ya kare ƙasarsa a game da zargin cewa bata taɓuka abin a zo a gani ba wajen cafke Osama bin Laden. Zargin ya zo ne bayan da dakarun sojin musamman na Amirka suka kashe shugaban na Al-Qa'ida a daren ranar lahadi. Murnar da manyan jami'an Amirka suka fara nunawa nan da nan ta sauya zuwa wani yanayi na ɗaure kai da kuma al'ajabi inda suke mamakin yadda mutumin da aka kwashe tsawon shekaru ana nema ruwa a jallo ya zauna daura da babban barikin sojin Pakistan kusa da babban birnin Islamabad ba tare da sanin mahukuntan ƙasar ba. Shugaban ƙasar ta Pakistan Asif ALi Zardari ya shaidawa jaridar Washington Post ta Amirka cewa ba tare da jami'an tsaron Pakistan aka kai farmaki akan bin Laden ba, sai dai kuma bai yi wani ƙarin haske ba akan yadda bin Laden ya zauna a ƙasar ba tare da mahukuntan sun sani ba. Shima Ministan harkokin wajen Pakistan ɗin Sal Bashir wanda ya gana da takwarorinsa na Amirka da kuma Afghanistan a birnin Kabul ya ƙi cewa uffan ko kuma yin ƙarin haske kan yadda aka kashe Osama Bin Laden. Shima Jakadan Amirka a Afghanistan Marc Grossman ya yi watsi da zargin cewa Gwamnatin Pakistan ta taimakawa Bin Laden samun maboya a cikin ƙasarta.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Ahmad Tijani Lawal