Martanin Putin ga Amurka
April 26, 2007Talla
Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya maida martani ga shirin Amurka na kafa cibiyar kariyar makamai masu linzami a ƙasashen Poland da jamhuriyar Czech. Vladimir Putin ya jingine hurumin Rasha a yarjejeniyar kariyar makamai da tarayyar turai. Yarjejeniyar wadda aka sanyawa hannu a shekarar 1990 ta tsaida waádi kan yawa da kuma samfurin makaman nukiliya da kowace kasa zata iya jibgewa a kan tsohuwar iyakar kasashen biyu. A jawabin sa ga majalisar dokokin Rasha, Putin ya soki lamirin yammacin turai yayin da a waje guda ƙungiyar tsaro ta NATO ke gudanar da taro a birnin Oslo domin tattauna harkokin tsaro a Afghanistan da kuma Kosovo.