Martanin ramuwar gayya a Afirika ta Kudu.
February 25, 2017Hare-haren nuna kyama da suka faru a kasar Afirika ta Kudu a wannan karon sun yi wa jama'a da dama zafi a Najeriya duk kuwa da matakan da mahukuntan kasar suka dauka na bayyana cewar suna tuntubar juna a mataki na diplomasiyya.Sanin cewa ba wannan ne karon farko da wannan ta taba faruwa.
Matasan dai na masu nuna gazawar daukar matakai daga banagaren gwamnatin Najeriyar amma minsitar kasa a ma'aikatar kula da harkokin kasashen wajen Najeriyar Sanata Hon Khadija Bukar Abba Ibrahim ta ce suna daukan mataki a kan lamarin.A yayin da ‘yan sandan Najeriya suka gargadi duk masu kai hare-haren ramuwar a Najeriyar,matasan tuni suka yi kawanya a gaban ginin MTN da ma sauran kamfanonin da suke mallakar kasar Afirika ta Kudu a yanayi na jiran kadan,ya zuwa yanzu dai ana sa ido don ganin mataki na gaba da gwamnatin Najeriyar za ta dauka a kan wannan lamari.