1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Afrika ta Kudu a kan ganawar Trump da Ramophosa

Zainab Mohammed Abubakar
May 22, 2025

Al'ummar Afirka ta Kudu sun soki abun da suka kira "ikirari mara tushe na shugaban Amurka na kisan kiyashi kan manoma farar fata" da aka yi ta maimaitawa a taronsu da shugaba Cyril Ramaphosa.

Hoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Ganawar da shugabannin biyu suka yi a jiya Laraba na da nufin gyara alakar da ta yi tsami tun bayan da Donald Trump ya hau karagar mulki a watan Janairu, inda daga baya ya yi barazanar kakaba harajin kasuwanci da kuma korar jakadan Afirka ta Kudu.

A yayin taron dai an nuna wani faifan bidiyo wanda ya nuna shugaban wata jam'iyyar adawa mai tsatsauran ra'ayi yana rera wakar gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata,.

Trump ya kuma sake nanata zarge-zargen da ba shi da tushe balle makama da ke cewa Afirka ta Kudu na kwace filaye daga wasu tsirarun fararen fatar kasar, zuriyar mazauna kasar Holland, wadanda a zahiri ke mallakar fiye da kashi uku cikin hudu na filayen kasuwanci.

'Yan kasar da dama suka kalli tattaunawara kai tsaye, tare da yin alfahari shugaba Ramaphosa da da tawagarsa.