1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan kasa bisa dokar ta-baci

Al-Amin Suleiman MuhammedNovember 18, 2014

Bayan da gwamnatin ta sanar da tsawaita dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa al’ummar yankin sun bayyana shakku kan manufar kafa dokar

Nigeria Anschlag Bombe Explosion Selbstmordanschlag
Hoto: picture alliance/AP Photo

Majalisar tsaro ta Najeriya ce dai ta amince a kara tsawaita dokar ta-baci karo na hudu a jihohi uku wadanda ke fama da rikici Kungiyar Boko Haram. Ministan shari'a na Najeriya, Mohammed Bello Adoke wanda ya bayyana matsayin majalisar tsaron, bayan kammala taron a fadar shugaban kasar da ke Abuja, ya ce yanzu haka shugaban Goodluck Jonathan na shirin tura wa majalisar dokoki ta kasa domin amincewa da wannan bukata.

Yawancin al'ummar yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana shakku da damuwa kan kara tsawaita wannan dokar ta-baci a kan cewar, ba zai cimma nasarar kafa ta ba. Malam Zakari Adamu shi ne shugaban Kungiyar Rundunar Adalci ta jihar Yobe.

Hoto: picture-alliance/dpa

Wasu al'ummar yankin dai sun bayyana fargabar cewar an dauki wannan mataki ne don hana yin zabubuka na shekara ta 2015 da ke tafe, kamar yadda Ahmadu Abacha Machina ya shaida wa DW.

Yanzu haka kuma akwai masu neman a dakatar da gwamnanin jihohin a nada kantomomin sojoji a yankin, lamarin da ake ganin ka iya hana gudanar da zabe a shekarar da ke tafe a wadan nan jihohin. Hon Mai Mala Buni, babban sakataren kasa na jam'iyyar adawa ta APC, ya ce ba za ta sabu ba bindiga a ruwa.

Su ma masu fafutukar kare hakkin jama'a kamar Abdullahi Inuwa, na ganin kamata ya yi gwamnatin ta aiwatar da aiyyuykan ta na samar da tsaro maimakon kara wa'adin dokar, inda ya ce hakan ba zai tsinana komai ba.


Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani