Martanin 'yan Nijar a kan ta'asar kamfanin Orano
December 3, 2025
Tun bayan da gwamnatin Nijar ta bankado labarin wasu tononuwa dari hudu masu dauke da guba da kamfanin ORANO ya binne a garin Madawaila cikin karamar hukumar Danet da ke gundumar Arlit a jihar Agadez, al'uma arewacin kasar da kamfanin ke wannan aikin suka soma tofa albarkacin bakinsu.
Madawaila, gari ne mai nisan kilomita 15 daga garin Arlit a cikin jihar Agadez, kuma a wani bincike gwmanatin mulkin soja ta ce ta binciko tare da gano gubar da kamfanin ORANO na kasar Faransa ya binne a can. Wannan labari ya tayar da hankalin al'uma.
Sai dai Ramar Ilatoufek, shugaban kungiyar farar hula ta Agarimen ya shaida wa DW cewa sun dade da fada wa gwamnatin wancan lokacin, batun gubar da ke jibge a garin na Madawaila.
Wasu dai na cewa, wannan aiki dai da kamfanin ORANO ya yi na hako sinadirin Uranium shekaru da dama da suka gabata bai amfani 'yan yankin da aka yi aikin da komai ba; sai ma tafiya da ya yi ya bar baya da kura, kamar yadda Amadou Idrissa Mahaman mai fafutukar kare muhalli a garin Arlit, shi ma yake ra'ayi.
A cewar Goura Abdou Ouseini, wani jamiin kwana-kwana da ke aiki a kamfanin Somair, suna farin ciki sosai da kasar Nijar ta kai karar ORANO don a kwato wa 'yan kasa hakkinsu, musamman ma al'umar da ke rayuwa cikin jihar Agadez inda ake wannan aiki na tonon sinadirin na Uranium.
Su dai al'uma arewacin Nijar na fatan ganin gwmanatin kasar ta sanya ido sosai ga wadanda za a bai wa wannan aiki a gaba domin kiyaye matsaloli da kuma samun amfanin abin ga al'uma, in ji Elkonci Mohamed mazauni a garin Danet.