Shin rikicin gabashin Kwango zai kawo karshe?
December 5, 2025
An dai cimma yarjejeniyar zaman lafiyar karkashin jagorancin Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango Felix Tshisekedi, da na Ruwanda Paul Kagame da jami'ai daga wasu kasashen Afirka da suka halarci zaman taron a Washington na kasar ta Amurka.
Saka hannu kan yarjejeniyar
Fadar White House ta sanya hannu kan yarjejeniyar a matsayin yarjejeniya mai tarihi da Trump ya shirya. Wannan ya biyo bayan watanni na kokarin zaman lafiya da Amurka da abokan huldarta suka yi, ciki har da Tarayyar Afirka da Katar. A fagen daga a garin Goma, inda aka shafe shekaru da dama ana yin yaki mazaunan yanki na yin gargadin cewa sai an yi taka tsantsan da yarjejeniyar.
'Yan tawayen da Ruwanda ke marawa baya sun mamaye Goma tun farkon wannan shekarar. Kungiyar M23 ta kwace manyan biranen yankin na Goma da Bukavu abin da ya kawo tsaiko kan al'amuran kasuwanci sufuri da sauransu. Ceslestin wani dan kasuwa a yanki ya ce suna fatan al'amura za su gyaru da wannan yarjejeniya.
Makomar wadanda suka tsere daga gidajensu
Ganin yadda miliyoyin mutane suka rasa matsugunansu abubuwa sun ƙara ta'azzara a gabashin Kwangon. A halin da ake ciki manyan biranen gabashin ƙasar na fama da matsalar rashin tallafin jinkai,babu asibitoci ga karancin magunguna da tsadar abinci.
Babbar ayar tambaya dai yanzu ita ce 'yan tawayen za su ɓace su ajiye makamai, za a dawo da ikon gwamnati a yankunan da 'yan tawayen suka kwace, an dai dade ana kokarin cimma yarjejeniyar zaman lafiyar tsakanin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da Rwanda a birnin Doha na kasar Katar amma lamarin ya gagara. Kawo yanzu dai kowa ya kasa kunne ya ji ko karan bindigogi za su tsaya a gabashin Kwango bayan wannan yarjejeniya.