1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martin Schulz zai zama babban kalubale ga Angela Merkel

Abdourahamane Hassane MNA
March 20, 2017

Da goyon baya 100 bisa 100 jam'iyyar SPD a Jamus ta zabi Martin Schulz a matsayin wanda zai kalubalanci shugabar gwamnati a zaben watan Satumba.

Deutschland SPD-Bundesparteitag in Berlin
Hoto: Reuters/A. Schmidt

A taron fidda gwani da ta gudanar a karshen mako, jam'iyyar SPD ta zabi Martin Schulz a matsayin dan takarar da zai kalubalanci shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, kana kuma shugaban jam'iyyar ba tare da fuskantar wani dan takara ba, wanda shi ne irinsa na farko da ya samu gaggarumin rinjaye.

Martin Schulz dan shekaru 61 da haifuwa tsohon kakakin majalisar tarrayar Turai, ilahirin wakilan jam'iyyar ta SPD sun kada masa  kuri'a domin jagorancin jam'iyyar ba tare da fuskantar takara daga wani da ke adawa ba. Kuma wannan shi ne karo na farko da jam'iyyar ta yi irin wannan zabe wanda ya zarta wanda aka taba yi wa Kurt Schumacher wanda ya samu kishi 99.71 cikin 100 a 1948 yayin da shi Martin Schulz ya samu dukkanin kuri'u 605 wato kashi 100 cikin 100.

Tafi da sowa sun barke dangane da goyon bayan da Schulz ya samu a taron jam'iyyar SPD Hoto: Reuters/F. Bensch

Jim kadan bayan an zabeshi, Martin Schulz ya yi jawabi yana mai cewa:

"Tare da ni babu wani fargaba a game da manufofin da aka saka ma gaba na karfafa kungiyar tarrayar Turai, sai dai kuma za mu bi duk hanyoyin da suka dace da samar da ci gaba da kuma hakin kasa don kyautata makomar bayanmu da wadanda za su gajemu a gaba.''

Schulz ya dai maye gurbin Sigmar Gabriel, wanda yanzu yake rike da matsayin ministan harkokin waje na Jamus wanda kuma ba shi da kwarjini sosai a idon jama'a lokacin da ya rike mukamin shugaban jam'iyyar ta SPD.

Ko Schulz zai iya kada Merkel?

Tun farko dai an yi tsammanin cewar game da irin yadda Martin Schulz ya kwase shekaru biyar yana aiki a matsayin shugaban majalisar tarayyar Turai a Brussels, hakan na iya zama cikas a gareshi wajen samun matsayin na shugaban jam'iyyar ta SPD. Sai dai kuma da yawa daga cikin magoya bayan jam'iyyar na ganin cewar shi kadai ne ke iya kakkabe shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel a zaben da ke tafe na watan Satumba, wacce siyasarta ta karbar 'yan gudun hijira ta janyo mata kaurin suna daga jama'ar kasar, wadanda ke neman maraba da ita.

Zaben watan Satumba: Merkel ko Schulz?Hoto: picture-alliance/dpa/G. Fischer

A yanzu haka dai hasashen da aka gudanar gabannin zaben da ke tafe na nuna cewar jam'iyyar CDU ta Angela Merkel tana kankankan da jam'iyyar SPD, har ma kusan SPD ta zartata.

Jannek Bruno Werner sabon memba ne a kwamitin gabatarwa na jam'iyyar ta SPD da ya yi karin haske kamar haka.

"Lokaci ya yi na tantance aya da tsakuwa tsakanin jam'iyya ta 'yan mazan jiya da kuma mu 'yan SPD, wannan zabe na Schulz wata babbar nasara ce ga ci gaban demokaradiyya.''

Martin Schulz ya sha alwashin yin kwaskwarima ga tsarin daukar sabbin ma'aikata a Jamus wanda ake ta cece-kuce a kansa wanda tsofon shugaban gwamnati kuma dan jam'iyyar ta SPD Gerhard Schröder ya kaddamar tsakanin shekara ta 2003 zuwa 2005, wanda ko da shi ke ma tsarin ya taimaka wajen rage masu zaman kashe wando amma kuma ya janyo talauci a sahun ma'aikatan na wancan lokaci.