Shugaban Peru ya yi murabus
March 23, 2018Talla
Majalisar dokokin kasar Peru ta amince da murabus da Shugaban kasar Pedro Pablo Kuczynski ya yi, abin da zai share hanya ga mataimakinsa tsohon gwamna wani lardi Martin Vizcarra ya dauki madafun iko a wannan kasa da ke yankin Latin Amirka.
Kuczynski ya zama shugaban kasa na farko da ruwan rikicin zargin cin hanci da wani kamfanin Brazil ya yi awun gaba da shi. Sai dai sabon Shugaba Martin Vizcarra na kasar ta Peru yana da gagarumin kalubale a gaba kan yaki da cin hanci da daidaita tattalin arzikin kasar.