Marubucin waka Leonard Cohen ya mutu
November 11, 2016Talla
Fitaccen mawaki kuma marubucin adabi Leonard Cohen ya mutu a shekaru 82. Sanarwar da aka gabatar ta dandalinsa na sada zumunta, na bayyana mutuwar tasa a matsayin babban rashi a fannin harkokin shakatawa.
Sanarwat ta kara da cewar, za'ayi shirye-shiryen bizinarsa a birnin Los Angeles na Amurka. A watan Oktoban da ya gabata ne dai mawakin, wanda dan asalin kasar Canada ne, ya gabatar da kundin wakokinsa na 14.