1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Wasikun barazana na tsorata muslumi a Jamus

Christioph Strack, MAB
August 15, 2023

Masallatai da dama na fuskantar barazana a Jamus a yayin da hukumomin tsaro ke lalubo hanyoyin kare su. Sai dai al'ummar Musulmi na bayyana tsoro game da nuna bacin rai kan wannan matsala ta rashin tsaro.

Masallata a babban masallacin Kolon a Jamus
Babban masallacin Kolon a JamusHoto: Mesut Zeyrek/AA/picture alliance

Wasu Musulmin kasar Jamus sun shafe shekaru suna samun wasiku na barazana ga rayuwarsu ko wurarensu na ibada, inda na baya-bayannan ya kasance wacce aka aika wa masallatai a gundumar Osnabrück da ke arewacin kasar a farkon watan Agusta. Sai dai Kiristoci ma ba su tsira daga samun irin wadannan wasiku ba.

Daidai da wasu sassa na jihohin Lower Saxony da Hessen da Bavaria da Berlin ma, masallatai da wasu Musulmi sun sami takardar barazana a cikin 'yan shekarun nan.

Akwai yiwuwar adadin Musulmin da ake ma barazana a Jamus ya zarta wanda aka sani a hukumance, saboda  ba dukkaninsu ne ke shigar da kara gaban 'yan sanda ba. Cibiyar Musulunci ta tarayyar Jamus ta bayyana cewar barazanar da ake yi wa al'ummar Musulmi ba sabon abu ba ne. Wasu ma daga cikinsu barazanar an rubuta su ne da hannu.  Babban sakataren majalisar koli ta Musulmin Jamus Abdassamad El Yazidi ya ce ambato sunan kungiyar NSU a matsayin kanwa uwar gami na tada hankali Musulmi da dama a kasar.

Musulmi a lokacin sallar Idi a masallacin KolonHoto: Mesut Zeyrek/AA/picture alliance

"Kasancewar wadannan wasikun suna magana ne game da NSU, ya nuna cewa masu aikata laifin suna kallon akidarsu a matsayin abin koyi, suna son farfado da ayyukan ta'addanci na NSU kuma suna daukaka su, kuma dole ne mu yi adawa da hakan ta hanyar da ya kamata. Wakilan dukkan addinai da ma mutanen da ba su da addini, mu yi aiki a matsayin al'umma domin kada wannan ya sake faruwa."

Rundunar ‘yan sandan Jamus ta ce 18 daga cikin wasikun barazana da aka aika wa Musulmi tun daga shekarar 2018, suna da alaka da kungiyar NSU ta masu tsaurin ra'ayin rikau. Hasali ma dai, tsakanin shekara ta 2000 zuwa 2007, mambobinta sun kashe 'yan ci-rani tara masu kananan sana'o'i da wata ‘yar sanda daya.

Sai dai ba a kai ga warware wanda ke da alhakin jerin kashe-kashen gillar ba. Amma a shekarar 2011 ne aka kama wadanda ake zargi da aikata wannan laifin.

Jamus| Babban masallacin KolonHoto: Mesut Zeyrek/AA/picture alliance

Wata kungiyar kwararru mai zaman kanta ta gabatar da wani cikakken rahoton bayan bincike kan kiyayyar da ake yi wa Musulmi a Jamus bayan kusan shekaru uku na aiki, wanda ya ke cewa matsalar na dada yaduwa. Kwararrun sun bayar da shawarwari kusan 20 ga gwamnatin tarayya wadanda suka hada da nadin kwamishinan tarayya da zai yi yaki da kyamar da ake nuna wa Musulmi. Sai dai har yanzu ba a fara aiwatar da shawarwarin ba, a cewar Al-Yazidi wanda ya yi koke a kan wannan batu.

"Hakika, muna sa ran hukumomin tsaro za su ba da kariya a wuraren da lamarin ya faru. Amma abin da muka fi sa rai a irin wannan yanayi shi ne, sakamakon karuwar nuna kyama ga Musulmi, muna neman hadin kai, muna sa ran karin tausayawa, muna sa ran karin himma don daidaita rayuwar Musulmi a Jamus da kuma shigar da Musulmi a cikin zamantakewar al'ummar Jamusawa."

A halin yanzu dai, wakilan kungiyoyin Musulmi na bayyana ra'ayoyinsu mabambanta kan matakan da ya kamata a dauka don kare Musulmi da wuraren ibadunsu a Jamus.