1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta haramta buda baki a masallatai saboda Coronavirus

April 5, 2020

Hukumomi a kasar Masar sun sanar sun haramta taron  buda-baki da al'umma musulmi ke yi a lokacin azumin watan Ramadan.

Ägypten Ramadan Iftar Mahl
Hoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/A. Gomaa


Ma'aikatar kula da masallatai ta kasar ta ce ba za a ga irin haka a azumin bana ba, saboda takaita  yaduwar Coronavirus. Hukumomi sun yi kira ga attajirai cewa a maimakon su tara cincirindon jama'a a lokacin shan-ruwa, zai fi kyau attajiran su rarraba wa gajiyayyu kayan abinci ko kuma su rarraba wa jama'a tallafin kudi. 

A watan da ya gabata Masar ta sanar da rufe masallatai a wani mataki na dakile yaduwar Coronavirus wace kawo yanzu ta kama mutane 1,070 ta kuma yi sanadin mutuwar 71. Sai dai babu tabbas ko kasar za ta bude masallatai a watan azumin don yin sallar Tarawihi da sauran ibadu.