Masar: An daure masu kaifin kishin addini
September 24, 2018Kotun kolin kasar Masar ta tabbatar a wannan Litinin da hukuncin daurin rai da rai kan wasu masu kaifin kishin Islama guda 20 wadanda a baya kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke wa irin wannan hukunci bayan samunsu da laifin kisan wasu 'yan sanda 13 a lokacin tarzomar da ta biyo bayan tsige tsohon shugaban kasar Muhammad Morsi a shekara ta 2013 inda aka kashe mutane sama da 700.
Kotun ta Allah ya isa ta ce mutanen ba su kuma da wata dama ta iya sake daukaka kara a nan gaba kasancewa wannan shi ne karo na biyu kuma na karshe da doka ta bai wa mutanen na iya shigar da kara a gabanta.
Kazalika kotun ta daga ita sai Allah ya isa ta yanke hukuncin zaman akso na tsawon shekaru ashirin da biyar-biyar ga wasu mutanen 50, na shekaru sha biyar-biyar ga wasu mutanen 35 kana ta saki wasu kimanin 20.