Masar da Isra'ila sun yi musayar fursunoni
October 27, 2011Talla
Ƙasar Masar da Isra'ila sun kammala aiwatar da musayar fursunoni tsakaninsu, abinda ake ganin zai iya sassauta rashin jituwa dake tsakanin ƙasashen biyu. Isra'ila ta sako yan ƙasar masar 25 ya yinda ita kuwa aka sako mata wani haifaffen Amirka da yanzu ya zama ɗan Isra'ila, wanda jami'an tsaron Masar suka tsare da zargin leƙen asiri. Ɗan Isra'ilan ya sauka a filin jiragen saman Ben Gurion jim kaɗan bayan da 'yan ƙasar ta Masar suka isa ƙasar su. Musayar ta biyo bayan wanda aka yi tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa inda aka sako sojan ta Glad Shalit, ita kuwa ta amince da sakin Falasɗinawa sama da dubu ɗaya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi