Gobara ta tashi a cocin Kobdawa a Masar
August 14, 2022Talla
Rahotanni daga Masar na cewa fiye da mutane 40 sun mutu wasu 55 sun jikkata, sakamakon tashin gobara a wata majami'ar 'yan Kibdawa da ke birnin Giza a wajen Alkahira.
Kibdawa su ne mafi girma a cikin al'ummar Kirista a yankin Gabas ta Tsakiya, a kusan mutane miliyan 10 daga cikin adadin 'yan Masar miliyan 103.
‘Yan tsirarun dai sun sha fama da hare-hare tare da kokawa da nuna wariya a kasar Musulmi mafi rinjaye a arewacin Afirka, wadda ta fi kowacce yawan al'umma a kasashen Larabawa.