1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaMasar

Mai sabuwar dokar hayar Masar ta tanada?

Mahmud Yaya Azare LMJ
July 10, 2025

Miliyoyin masu haya a gidajen da aka kayyade musu farashi tun shekaru 70 da suka gabata a Masar, na fuskantar barazanar fitar da su da karfi daga gidajen.

Masar | Abdel Fattah al-Sisi | Doka | Gidajen Haya | Sabon Tsari
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-SisiHoto: JAVIER SORIANO/AFP/Getty Images

Wannan fargaba da mazauna gidan hayar ke ciki, na zuwa ne sakamakon wata doka da majalisar dokokin Masar ta amince da ita take jiran shugaban kasar ya rattaba mata hannu. Kimanin mutane miliyan 20 da ke zaune a gidajen haya kusan miliyan uku da a aka kayyade musu farashi tun shekaru 70 da suka gabata ne, wannan doka da ta yi gyaran fuska za ta shafa. A tsohuwar dokar haya da ake aiki da ita tun shekaru kimanin 70 din da suka gabata, mai haya a wancan lokacin zai bayar da makudan kudin da sun kai daya bisa ukun kudin gidan na hakika domin ya zauna a gidan shi da ya'yansa manya har iya bakin ransu yadda za su dinga biyan tabbataccen kudin hayar da bai taka kara ya karya a wancan lokacin ba ballantana a yanzu. Wafa Ashur da ta gaji daya daga cikin gidajen hayar da aka bayar da hayarsu a kan tsohon tsarin dokar haya ta ce, idan wannan dokar ta fara aiki za ta fara karbar kudin hayar da suka dace da darajar gidanta ko kuma a ba ta damar komawa gidan ta zauna bayan fitar da 'yan hayar cikinsa.

Gwamnati dai ta ce za ta rarraba sababbin gidaje ga wadanda suka yadda suka bar tsofafin gidajen da suke biyan kudin hayar jeka-na-yi-kan da bai karuwa tun shekaru 60, idan suka fita daga gidajen domin radin kansu a kokarin da take ta raba gardama tsakanin masu gidajen hayar da 'yan hayar da kowannansu ke zargin cewa ana so ne a cuce shi. To sai dai da dama daga cikin 'yan hayar sun dage kan cewa, ba za su bar cikin birni da suka rayu shekara da shekaru ba. Shi kansa Shugaba Abd al-Fattah al-Sisi da ake jiran ya ranttaba hannu a kan wannan sabuwar doka ya ce, dola ce ta sanya shi daukar matakin kawo karshen dokar gidajen hayar da ta jima tana janyo rikici tsakanin 'yan haya da masu gidajen hayar. Tun daga shekarar 1960 ne aka fara cin moriyar wannan tsarin hayar a kasar ta Masar, wadda kuma ke janyo cece-kuce.