Masar: Shekaru 8 da kadawar guguwar neman sauyi
January 25, 2019An wayi gari da wakar jinjina ga 'yan sandan Masar da rundunar sojin kasar ta sadaukar musu a bikin shekara shekara na bana da ake yi albarkacin sadaukar da rana da ta ce anyi don tabbatar da zaman lafiya da murkushe boren neman sauyin da Shugaban kasar Abdel-Fatah al-Sisi ya siffanta da wata mummunar katobara a tarihi.
'Yan sandan da dama ake ganin sune dalilin barkewar zanga zangar da ta kai da yin awon gaba da mulkin Shugaba Hosni Mubarak, a yanzu ranar juyin juya halin na Masar, ya rikide ya zama ranar bikin tunawa da gudummawar da suke bayarwa wajen tabbatar da tsaron al'umma, a yayin da galibin wadanda suka yii boren 2011, ko dai an kashesu ko kuma suna daure ko sun tsere daga kasar, ko kuma sun bace a rububi, lamarin da ya sanya wasu 'yan kasar ke cewa, dama can boren neman sauyin muguwar rawace, da ake cizan yatsa kan tashi a ayita.
Kasancewar ranar tunawa da juyin juya halin na Masar a bana ya zo ne a daidai lokacin da boren neman sauyi ya barke a a Sudan da ke makwabtaka da kasar. Ya sanya mahukuntan na Masar daukar tsauraran matakan tsaro, kamar yadda tawagar jami'an leken asirin Masar ta je birnin Khartoum don bai wa mahukuntan Sudan shawarwari kan matakan da ake bi a murkushe irin wannan boren.