1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Sabon fata bayan shiga BRICS daga Masar

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2023

Masar na fatan shigarta cikin kungiyar Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Bunkasa Cikin Hanzari wato BRICS, zai taimaka wajen shawo kan matsalar karancin kudin kasashen ketare da take fama da ita.

Afirka ta Kudu | Johannesburg | BRICS | Taro
Sababbin mambobin kungiyar BRICS na da kyakkyawan fataHoto: Sergei Bobylev/TASS/dpa/picture alliance

Masar din dai, na kuma fatan shigarta kungiyar ta BRICS ka iya yi mata zabarin masu zuba jari. Sai dai kwararru na bayyana cewa, zai dauki lokaci kafin Masar din da sauran sababbin mambobin BRICS din su fara cin gajiyar shiga kungiyar ta BRICS. Masar dai na daga cikin kasashe shidan da kungiyar da ta kunshi kasashen Brazil da Rasha da Indiya da Chaina da kuma Afirka ta Kudu, ta amince da shigar su cikinta a yayin taronta da ta kammala a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu. Sauran kasashen da suka samu tagomashin shiga cikin BRICS din sune: Saudiyya da Iran da Ajantina da Habasha da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.