Hadarin jirgin kasa ya yi sanadiyar mutuwar mutum 25
February 27, 2019Talla
Jirgin dai ya saki hanya kafin ya daki wani shinge da ke tashar jirgin, bayan nan an yi ta jin fashewa da hayaki da ya turnuke iska. Lamarin ya haifar da rudani. A jawabin Firaiministan kasar Mostafa Mad-bouly, jim kadan bayan aukuwar lamarin, ya ce za su gudanar da bincike kuma za a hukunta duk wani wanda ke da hannu in har an tabbatar an kitsa hadarin ne da gangan. Babu dai tabbaci daga hukumomi ko yana da nasaba da ayyukan ta'addanci.
Yanzu haka kuwa rahotannin da ke shigo mana daga kasar Mali na nuni da cewa, mutum akalla goma sha bakwai sun mutu a wani cunkoson jama'a.