Masar na son a kara tasirin Afirka a kwamittin sulhu na MDD
December 21, 2025
Shugaba Abdel-Fattah el-Sissi na Masar ya bukaci a kara tasirin nahiyar Afirka a cikin kwamittin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron hadin gwiwar Rasha da kuma Afirka da ya gudana a birnin Alkahira. Taron da ya samu halarcin ministan harkokin kasashen wajen Rasha, Sergey Lavrov da kuma wasu ministoci daga kasashen Afirka fiye da 50.
El-sissi ya ce akwai bukatar muryar Afirka ta kara yin tasiri sosai, yana mai cewa, nahiyar na da yawa jama'a da tattalin arziki da girman siyasar da ma alumomi.
Karin bayani: Matsayin Afirka a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya
Tun dai a shekarar 2005 ne, Kungiyar Tarayyar Afirka AU ke neman a bai wa nahiyar Afirka a kalla kujeru biyu na dindindin da kuma karfin iko a kwamittin sulhu. A yanzu dai kasashen China da Amurka da Rasha da Burtaniya da Faransa ne ke da kujeru na dindindin a kwamittin.