Masar ta kalubalaci alkalin FIFA
July 9, 2026
A cikin wata sanarwa, hukumar ta ce wasu muhimman hukunce-hukuncen da alkalin ya dauka da kuma yadda aka yi amfani da fasahar VAR sun yi tasiri kai tsaye kan sakamakon wasan da aka tashi 3 da 2. Ta bayyana cewa irin wadannan matakai sun haifar da shakku kan adalci da daidaito kan alkalancin wasan.
Tun da farko, kocin Masar, Hossam Hassan, da wasu daga cikin 'yan wasan sun soki yadda aka tafiyar da shafa leda, musamman bayan soke kwallo da Masar ta zura a raga bayan sake duba fasahar mataimakin alkali wato VAR, tare da kin ba ta bugun fenariti a inda ya yakamata.
Hukumar kwallon kafar Masar ta kuma sanar da cewa ta shigar da korafi a hukumance ga FIFA, tana neman a binciki yadda alkalin wasan ya gudanar da aikinsa, tare da bukatar hana shi hura sauran wasanni a gasar. Sai dai har zuwa yanzu, FIFA ba ta fitar da wata sanarwa kan korafin da Masar ta shigar ba, yayin da Argentina ke ci gaba da shirye-shiryen fafata wasan daf da na kusa da na karshe.