Masar ta katse ba da makamashi ga Israi' la
April 23, 2012An samu kunnowar sabuwar takkadama tsakanin Masar da Isra'ila bayan da kamfanin gas din kasar Masar ta sanar da ske yarjejeniyar da ta kulla tare Isra'ila akan cinikin gas. Shi dai kamfanin gas din ya bayyanar da rashin biye wa yarjejeniyar a matsayin dalilinsa na daukar wannan mataki. Hakazalika ma'aikatar man fetur kasar ta Masar ta sanar da dakatar da ba wa Isra'ila mai a sakamakon abin da ta kira hare-haren da ake zargin kungiyoyin kishin Islama da kaiwa akan bututan mai da ke a yankin Sinai. Kasar Masar ita ce ke samar wa Isra'ila kashi 40 daga cikin dari na iskar gas da take bukata. Tuni jami'in gwamnatin Isra'ila ya yi kashedi game da katsewar wutar lantarki a lokacin rani .
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala